A yau Alhamis, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabi na musamman ga al’ummar Najeriya, domin bikin cika shekaru 66 da samun ‘yancin kan kasar, inda ya sanar da cewa kasar ta riga ta tsallake matakin dokar ta baci a fannin tattalin arziki.
Shugaban ya bayyana cewa tsauraran matakan gyara da gwamnatinsa ta dauka a baya sun kammala aiki, kuma a yanzu Najeriya ta shiga sabon babi na wadata da ci gaba ga daukacin ‘yan kasa.
A cikin jawabin, wanda aka watsa kai tsaye a kafafen yada labarai na kasar, Shugaba Tinubu ya amince da kalubale da matsin rayuwa da al’umma suke fuskanta. Sai dai ya jaddada cewa wadancan tsauraran matakan sun zama dole domin ceto kasar daga rugujewa,
Shugaban ya bayyana nasarorin da aka samu na farfadowar tattalin arziki a cikin shekarar 2026, ciki har da bunkasar tattalin arziki da ya wuce kashi hudu cikin dari, daidaituwar farashin canjin kudaden waje, da kuma raguwar hauhawar farashin kayayyaki.