Korarren ministan tsaron Isra’ila ya mika takardar yin murabus dinsa daga majalisar Dokokin Knesset kuma ya zargi Netanyahu da yin barazana ga tsaron sojojin kasar
Tsohon ministan yakin gwamnatin mamayar Isra’ila Yoav Gallant ya sanar da yin murabus daga majalisar dokokin haramtacciyar kasar Isra’ila ta “Knesset”, lamarin da ke nuni da cewa nan ba da jimawa ba, zai mika takardar murabus dinsa ga shugabancin majalisar.
A cikin wani jawabi mai ban mamaki, da ya gabatar a yammacin jiya Laraba, Gallant ya yi kakkausar suka ga Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila, Benjamin Netanyahu, yana zarginsa da yanke shawarar da ke barazana ga tsaron “Rundunar Sojan Isra’ila.”
Yana mai cewa: Fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila ya kore shi ne saboda ya fifita muradun Isra’ila sama da komai, wanda ya Sanya Netanyahu ya sallame shi daga matsayin ministan tsaron Isra’ila.
Gallant ya kara da cewa: Daukar yahudawan sahayoniyya na Haredim ba batu ne na siyasa kawai ba, a’a yana bukatar tsaro ta asali don tabbatar da zaman lafiyar sojojin mamayar Isra’ila da kuma karfinsu na tunkarar kalubale.