Tashar talbijin din “almayadeen” mai watsa shirye-shiryenta daga Beirut na kasar Lebanon ta ambato tsohon kwamandan yankin tsakiya dake kusa da Gaza na HKI; Janar Gadi Shamni yana yin gargadi akan abinda ya kira; Barazanar da Iran ta yi, tare kuma da yin ishara da sabanin dake tsakaninsu da Amurka.
Janar Gadi Shamni ya ce; Dole ne gwamnati da sojojin Isra’ila su dauki barazanar da ta fito daga wakilin Iran a MDD dangane da yakin Lebanon da gaske.
Janar Shamni ya kuma bayyana sabanin da yake a tsakanin Isra’ila da kuma Amruka, tare da cewa, ba domin taimakon da suke daga Amurka ba, to da sun fuskanci wahalhalu masu yawa.
Ofishin wakilcin Iran a MDD ya rubuta a shafinsa na X cewa; Idan har yake ya barke da Lebanon, to dukkanin kawancen gwgawarmaya zai shiga ciki da karfinsa.”