Iran Ta Kira Mai Wakiltan EU A Tehran Don Gabatar Da Korafinta Kan Takunkuman Tattalin Arziki Da Ta Dorawa Kamfanin Jiragen Ruwan Kasar

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kira jakadan kasar Hungary a Tehran zuwa ma’aikatar a ranar Talatan da ta gabata don gabatar da korafinta ga

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kira jakadan kasar Hungary a Tehran zuwa ma’aikatar a ranar Talatan da ta gabata don gabatar da korafinta ga kungiyar Tarayyar Turai wacce ta dorawa kamfanin zirga zirgan jiragen ruwa na kasar takunkuman tattalin arziki kan wasu dalilai marasa tushe.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa ma’aikatar ta jakadan Hungary a nan Tehran, wanda yake wakiltan kungiyar a shugabancin karba karba na kungiyar a nan Tehran, zuwa ma’aikatar harkokin wajen kasar da ke Tehran don gabatar da korafinta ga kungiyar, dangane da sabbin takunkuman tattalin arziki wadanda kungiyar ta EU da kuma kasar Burtaniya suka dorawa wasu daddaikun mutane, da kuma kamfanoni wadanda suka hada da kamfanin zirga zirgan jiragen ruwa na kasar Iran a cikin yan kwanakin da suka gabata.

Labarin ya kara da  cewa kungiyar EU da Burtania sun dorawa kasar Iran sabbin takunkuman tattalin arziki ne da sunan wai JMI ta aikawa kasar Rasha makamai a yakinta da ukraine.

Majdi Nili daraktan mai kula da al-amuran yammacin Turai a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya musanta zargin kasashen na turai a gaban jakadan kasar ta Hungary, ya kuma bayyana cewa zargin bai da toshe ballanta makama.

Kafin haka dai jami’an gwamnatin kasar Ukraine sun tabbatar da cewa zargin kasashen na Turai kann JMI ba gaskiya bane. Amma wadannan kasashe sun yi kunnen uwan shego da rahoton Ukraine.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments