Sojojin Yemen Sun Kwace Wani Jirgin Ruwan HKI A Sabon Kokari Na Tallafawa Falasdiawa

Sojojin kasar Yemen sun kwace wani jirgin ruwan HKI a cikin tekun Maliya a wani sabon yunkuri na taimakawa Falasdinawa a Gaza, wadanda suke fafatawa

Sojojin kasar Yemen sun kwace wani jirgin ruwan HKI a cikin tekun Maliya a wani sabon yunkuri na taimakawa Falasdinawa a Gaza, wadanda suke fafatawa da sojojin HKI fiye da watanni 13 da suka gabata.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar sojojin kasar Yeman na fadar haka a jiya Laraba, ta kuma kara da cewa, ta kama ma’aikatan jirgin kuma tana kula da su kamar yadda addinin musulunci ya bukaci a kula da fursinonin yaki.

Labarin ya kara da cewa sojojin kasar sun kama jirgin ruwan da kuma ma’aikatansa ne tare da umurnin shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi, saboda tallafawa Falasdinawa a Gaza wadanda Amurka da HKI sukewa kissan kiyashi fiye da shekara guda da ta gabata.

Ya zuwa yanzu dai Falasdinawa kimani dubu 44 ne sojojin HKI tare da tallafin Amurka suka kai ga shahada daga ranar 07 ga watan Octoban shekara ta 2023.

Tun farkon yakin ne, sojojin Yemen suke kai hare hare kan jiragen ruwan kasuwanci mallakin  HKI da masu goya mata baya wato Amurka da Burtani a tekun Maliya, da Tekun Aden da Tekun Arabia.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments