Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye ta bayyana cewa manufar HKI a yakin da take fafatawa da Falasdinawa a Gaza tun ranar 07 ga watan Octoban shekara ta 2023 ita ce ganin cewa babu wani bafalasdine da ya rage a cikin kasarsu da aka mamaye, Sannan ta gina matsugunan yahudawa a duk fadin kasar Falasdinu da ta mamaye.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani babban jami’in kungiyar ta Hamas yana fadar haka a jiya Laraba. Khalil Al-Hayya ya fadawa tashar talabijin ta Al-aksa kan cewa yahudawa Sahyoniyya basu bar kawo daga cikin Falasdinbawa ba. Kuma suna kashe mata da yara da tsoffi da duk wanda ya kasance bafalasdinu a yankin Gaza don cimma wannan manufar.
Al-Hayya ya bayyana haka ne a daidai lokacinda yawan Falasdinawa da suka kai ga shahada tun ranar 07 ga watan Octoban shekara ta 2023 ya kusan kaiwa dubu 45. Jami’in yace mafi yawan wadanda aka kai su ga shahadan mata da yara ne.
Al-Hayya ya kara da cewa kissan kiyashin da HKI tare da tallafin gwamnatin Amurka suke yi a gaza, shi ne kissan kiyashi mafi muni a wannan zamanin. Kuma suna aikata hakan ne a gaban idan kasashen duniya ba tare da samun wanda ya isa ya dakatar da su.
Har’ila yau a jiya Laraba ce, gwamnatin kasar Amurka ta hana kudurin kwamitin tsaro na MDD karo na 7 dangane da tsagaita wuta a Gaza wucewa a kwamitin tsaro. Wannan yana faruwa ne bayan da dukkan mambobin kwamitin tsaron 14 sun amince da shi.