Babban Sakataren Kungiyar Hizbullah Na Kasar Lebanon Ya Ce HKI Zata Yi Nadamar Hare Haren Da Take Kaiwa Kan Birnin Beirut

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanin Sheikh Na’im Qasem ya bayyana cewa HKI zata ji ba dadi saboda hare haren da take kaiwa kan

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanin Sheikh Na’im Qasem ya bayyana cewa HKI zata ji ba dadi saboda hare haren da take kaiwa kan birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Sheikh Qasem yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Laraba. Ya kuma yi ta’aziyyar shahidan kungiyar da masu gwagwarmaya a yankin, wadanda suka hada da babban sakataren kungiyar marigayi Sayyeed Hassan Nasarallah, da Hashem Safieddine, Janar  Qasim Soleimani, da kuma shugaban bangaren yada labarai na kungiyar Mohammad Afif al-Nabulsi a baya bayan nan.

Sheikh Qasem ya bayyana cewa kissan Muhammad Afif Annablusi ba zai wuce ba tare da kungiyar ta maida martani kan birnin Tel-Avivb ba.

A wani bangare na jawabinsa shugaban kungiyar ta Hizbullah ya godiya kasashe da kungiyoyi wadanda suke tallafawa juna a kawancen masu gwagwarmaya a yankin. Wadanda kuma suka hada da kasashen Yemen, Iraki, JMI da Gaza. Ya kuma roki All..ya jikan shahidan wadannan kasashe da kungiyoyi wadanda suka yi shahada a cikin watanni kimani 13 da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments