Iran Da Qatar Sun Sha Alwashin Gaggauta Aiwatar Da Yarjejeniyoyin Da Suka Cimma

Kasashen Qatar Da Iran sun tattauna kan batutuwa da dama ciki har da halin ha ake ciki a yankin. Wannan bayannin ya fito bayan da

Kasashen Qatar Da Iran sun tattauna kan batutuwa da dama ciki har da halin ha ake ciki a yankin.

Wannan bayannin ya fito bayan da tattaunawar data wakana tsakanin shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkina da Firaminista, kuma ministan harkokin wajen Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani a ziyararsa Tehran.

Bangarorin sun bayyana mahimmancin gaggauta aiwatar da yarjejeniyoyin da suka kulla a baya.

Shugaba Pezeshkian ya jaddada manufarsa ta hadin kai a tsakanin kasashen musulmi, yana mai cewa, “Muradinmu na hakika shi ne kulla alaka ta kut da kut da ‘yan uwanmu musulmi da kuma nuna wa duniya cewa kasashen musulmi za su iya rayuwa tare cikin aminci da lumana, da mutunta juna.”

A nasa bangare firaministan na Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, a yayin da yake bayyana muradin kasarsa na fadada alaka da Iran, ya bayyana “Sarki da gwamnatin Qatar sun jajirce wajen gaggauta aiwatar da yarjejeniyoyin da aka kulla a tsakanin kasashen.

Qatar da Iran sun kuma tattauna kan Halin Da Ake Ciki A Yankin musamman a Gaza da Lebanon.

Qatar ta kasance babbar mai shiga tsakani a tattaunawar da aka yi da nufin samar da tsagaita wuta a Gaza da kuma sakin fursunonin Isra’ila tun watan Oktoban 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments