HKI: Sojojin Kasar Na Dab Da Rushewa

 Wani babban kwamandan sojojin HKI mai ritaya Ithak Brik ya bayyana cewa, mayar da kasar saniyar ware da kasashen duniya suke yi ya kai matsayinda

 Wani babban kwamandan sojojin HKI mai ritaya Ithak Brik ya bayyana cewa, mayar da kasar saniyar ware da kasashen duniya suke yi ya kai matsayinda kasar ba zata iya jurewa ba, don haka akwai yiyuwar rundunar sojojin kasar tana iya rushewa a kao yaushe.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Brik yana fadar haka a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa, gwamnatin haramtacciyar kasar tana fama da matsaloli wadanda maida ita saniyar waren da kasashen duniya suke yi, daga ciki har da kawayenta, ya sanya ba zata iya jurewa wannan kauracewar na lokaci mai tsawo ba.

Sawa’un a bangaren tsaro, tattalin arziki da kuma cibiyoyin gudanar da kasar ne. A wani bayanin da jiridar Maariv ta haramtacciyar kasar ta buka, ta nakalto Brik yana cewa, sakamakon zaben ranar talatan da ta gabata, ya na dai dai ta fidda takardar shaidar wargajewar kasar ne. Ya zargi kafafen yada labaran yahudawan na boye gaskiya, maida hankali kan kokarin samar da hadakar kafa gwamnati, ba tare da raunin da ke fuskantar bangarorin gudanarwa na kasar ba.

Ya ce, HKI tana cikin matsalolin siyasa, wannan gaskiya ne, amma tana fuskantar matsaloli mafi hatsari da ta siyasa, kuma sun hada da rugujewar tsarin tafiyar da gwamnatin kasar saboda maida ita saniyar ware da ake yi kuma ake kara yi a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted