Tsagerun yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida sun kutsa cikin Masallacin Al-Aqsa tare da kariyar ‘yan sandan h.k.Isra’ila
Shaidun ganin ido sun bayyana cewa: Wasu tsagerun yahudawan sahayoniyya da dama sun kutsa cikin harabar Masallacin Al-Aqsa mai albarka da ke birnin Qudus, karkashin kariyar ‘yan sandan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.
Kutsen tsagerun yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida ya gudana ne rukuni-rukuni ta hanyar kofar Mughgariba, inda suka gudanar da rangadi na tsokana tare da gudanar da ibadar Talmud a cikin harabar Masallacin.
‘Yan sandan gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar ta Isra’ila sun kuma tsaurara matakan tsaro a kofar tsohon birnin da masallacin na Al-Aqsa.