Trump Ya Yi Wa Kungiyar “Brics” Barazanar Rushewa

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi wa kungiyar Bricks barazanar cewa za ta rushe idan har ta yi kokarin zama mai karfin tasiri. Trump

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi wa kungiyar Bricks barazanar cewa za ta rushe idan har ta yi kokarin zama mai karfin tasiri.

Trump ya ce, lokacin da fara jin labarin wannan kungiyar da ta kunshi kasashe 6, na bude fada da su cikin karfi, kuma za rushe cikin sauri, idan ta yi kokarin zama mai karfin tasiri.”

Shugaban kasar ta Amurka  ya kuma ce; Wajibi ne a kaina in kare karfin kudin Dala a duniya domin shi ne kudin da ake amfani da su a matsayin na ajiya, ba kuma zan taba bari a kafa Bankunan kudaden yanar gino na lambobi,a cikin Amurka.

Shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya kuma ce, duk wata kasa wacce take dasawa da “Brics” to za a kara mata kudaden fito.”

Ita dai kungiyar Brics wacce ba ta dade da kafuwa, ta zama mafakar da kasashe suke komawa gare ta, bayan da sauran kungiyoyin da ake da su irin su G-7 da G-20 suke tasirantuwa da shiftar Amurka.

Shugaban kasar na Amurka ya sha bayyana cewa, kungiyar Brikcs tana son rage karfin tasirin Dalar Amurka a duniya.

Shugabannin kungiyar ta Brics dai sun yi watsi da tuhume-tuhumen da Shugaban na kasar ta Amurka take yi musu.

Shugaban kasar Brzil  Lula Da Silva  wanda ya gabatar da jawabi ta kafafen watsa laabrun kasar a ranar Alhamis din da ta gabata, ya bayyana barazanar ta Trump da cewa tsokana ce.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments