Unrwa Ta Sake Yin Kira Ga HKI Da Ta Bari A Shigar Da Kayan Agaji

Hukumar Agaji ta MDD mai kula da Falasdinu ( Unrwa) ta sake yin kira ga HKI da ta bari a shigar da kayan agijin da take da su masu yawa a jibge a yankin Arish na kasar Masar. Hukumar ta yi wannan kiran ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na X tana […]
Fadar Shugaban Kasar Syria Ta Sanar Da Tsagaita Wuta A Yankin Suwaidaa

A yau Asabar fadar shugaban kasar Syria ta sanar da tsagaita wutar yaki a Suwaidaa da ta yi fama da tashe-tashen hankula. A wani bayani da fadar shugaban kasar ta Syria ta fitar ya kunshi cewa An dauki wannan matakin ne na tsagaita wuta saboda an shiga wani yanayi mai hatsari a cikin kasar, da […]
Trump Ya Yi Wa Kungiyar “Brics” Barazanar Rushewa

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi wa kungiyar Bricks barazanar cewa za ta rushe idan har ta yi kokarin zama mai karfin tasiri. Trump ya ce, lokacin da fara jin labarin wannan kungiyar da ta kunshi kasashe 6, na bude fada da su cikin karfi, kuma za rushe cikin sauri, idan ta yi kokarin […]
Kudaden Da Iran Ta Samu Daga Hajar Da Ba Man Fetur Ba Sun Haura Dala Biliyan 11

Kididdgar da hukuma mai kula da shiga da ficen kaya ta Iran ta bayyana cewa, kudaden da kasar ta samu a watanni hudu na farkon shekarar Iraniyawa, ( Daga 20 ga watan Maris zuwa yanzu) sun kai dalar Amurka biliyan 11 da miliyan 655. Kamfanin dillancin labarun Mehr na Iran ya ambato hukumar shiga da […]
Kasar Iran Ta Bayyana Cewa: Zabinta Ne Daukan Matakin Da Ya Dace Idan Aka Sanya Mata Matsin Lamba

Kwamitin Tsaro na Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa; Zabin Iran ne ta daukin duk matakin da ya dace idan aka Sanya mata matsin lamba Kakakin kwamitin tsaron kasa da manufofin harkokin waje na majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran ya bayyana cewa: Ci gaba da matsin lamba da kasashen Turai ke yi […]
Jakadan Iran A Kasar Rasha Ya Ce: Sharuddan Sake Komawa Zaman Tattaunawa Da Amurka Ba Su Cika Ba

Jakadan Iran a kasar Rasha ya bayyana cewa: Sharuɗɗan sake tattaunawa da Amurka ba su cika ba Kazem Jalali, jakadan Iran a kasar Rasha ya bayyana cewa: A halin yanzu, bisa ga hujjojin da ake da su, ba a cika sharuddan sake tattaunawa da Amurka ba na kai tsaye ba, domin har yanzu Amurkawa ba […]
Babban Sakataren Kungiyar Hizbullahi Ya Ce; A Shirye Suke Su KaluBalantar Makiya Babu Batun Mika Kai

Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya jaddada cewa; A shirye suke su kalubalanci makiya, babu batun mika kai daga gare su Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Qasem ya bayyana a wajen taron tunawa da babban jagoran jihadi Hajj Ali Karaki (Abu al-Fadl Karaki) cewa: Shugaban da […]
Iran Ta Soki Matsayin Turai Na Yaudara Game Da Wuce Gona Da Iri Kan Kasar Siriya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta soki matsayin Turai na yaudara game da wuce gona da iri kan kasar Siriya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi tsokaci kan tsarin yaudara da zabin da kungiyar tarayyar Turai ke yi kan harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan kasar Siriya. Da yake mayar da martani […]
Gwamnatin Mauritaniya Ta Karyata Batun Ganawar Shugaban Kasar Da Fira Ministan Gwmanatin Isra’ila

Rashin amincewar gwamnatin Mauritaniya da al’ummar kasar da duk wani batun neman kyautata alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila Maganar neman kyautata alaka tsakanin yahudawan sahayoniyya da Mauritaniya ya haifar da cece-kuce da kwarara kan titin Mauritaniya, lamarin da ya sa gwamnatin kasar ta musanta hakan nan take. Kafofin yada labaran Amurka sun rawaito cewa, ganawar […]
Shiek Qasim: HKI Tana Son Lalata Iran Amma Ta Kasa Yin Hakan

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bayyana cewa HKI ta so ta lalata kasar Iran ta kuma kifar da gwamnatin JMI, amma ta kasa yin hakan da yardarm All.. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto babban sakataren kungiyar Sheik Naem Qasim yana fadar haka a jiya Jumma’a da yamma. Ya kuma kara […]
Makamai Masu Linzami Na Kasar Yemen Ta Fada Kan Tashar Jaragen Sama Na Ben Gurrion

Majiyar sojojin kasar Yemen ta bayyana cewa sojojin kasar sun cilla makamai masu linzami sanfurin Bilistic kan tashar jiragen sama mafi cinkoso da ke birnin Yafa ko Tel’aviv, wanda na farko ya tilastawa jiragen sauka da dashi a tashar. Sannan miliyoyin mutane suka ruga zuwa mabuya saboda tsaron kansu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar […]
Shugaban Mabiya Duruz A kasar Lebanon Yace Basa Bukatar Kariyar HKI

Sheikh Sami Abi al-Muna, shugaban kungiyar mazhabar Duruz a kasar Lebanon ya bayyana cewa jama’arsu basa bukatar kariya daga HKI, duk da cewa suna daga cikin kananan mazhabobin addinin musulunci a kasar ta Lebanon. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Abi-Almun yana fadar haka a taron da malamai da shuwagabannin mazhabar suka […]
Aragchi Yace Za’a Farfado Da Tattaunawa Da Amurka Ne Kawai Idan Tana Son Adalci ga Kasarsa

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa iran zata bude sabuwar kofar tattaunawa da Amurka ne kawai idan a shirye take da yi adalci babu takurawa daga kasashen yamma. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, kasashen yamma da Amurka da kuma kasashen yamma suna barazanar kara takurawa kasar […]
Iran, Rasha Da China Sun Fara Tattauna Batun Yakin Kwanaki 12 Da Amurka Da HKI Suka Dorawa Iran

Kasashen Iran, China Da rasha sun fara tattaunawa dangane da yakin kwanaki 12 wanda kasashen Amurka da HKI suka dora mata kan shirin ta makamashun Nukliyakasar. Kasashen uku suna son daukar mataki guda a kan abinda ya shafi wannan matsalar, saboda yadda HKI da Amurka suke yin abinda suka ga dama dangane da shirin makamashin […]