Trump ya yi barazanar korar Gwamnar Babban Bankin Amurka

Shugaba Donald Trump, ya yi barazanar sauke Lisa Cook, Gwamnar Babban Bankin Amurka (Federal Reserve), yana mai sukar yadda ake tafiyar da harkokin bankin, musamman

Shugaba Donald Trump, ya yi barazanar sauke Lisa Cook, Gwamnar Babban Bankin Amurka (Federal Reserve), yana mai sukar yadda ake tafiyar da harkokin bankin, musamman batun bayar da bashi da tsare-tsaren lamuni.

A wata sanarwa da fadar White House ta fitar, Trump ya zargi Cook da gabatar da “bayanan ƙarya” kan sharuɗan bayar da lamunin gidaje (mortgage), yana mai cewa hakan ya jefa dubban Amurkawa cikin wahala sakamakon hauhawar kuɗin ruwa da kuma tsadar bashi.

Sai dai Lisa Cook ta mayar da martani da cewa shugaban ba shi da ikon sauke ta daga muƙamin da take riƙe da shi, saboda dokar da ta kafa Babban Bankin Amurka ta tanadar da cikakken ’yanci ga ’yan kwamitin gudanarwarsa.

Ta sha alwashin cewa za ta ci gaba da gudanar da aikinta ba tare da wani ɗar-ɗar ba, tana mai cewa manufarta ita ce kare tattalin arziƙi da talakawan ƙasar.

Cook ta yi suna tun lokacin da tsohon shugaban Amurka, Joe Biden, ya naɗa ta a shekarar 2022, inda ta zama mace baƙar fata ta farko ’yar asalin Afirka da ta taɓa zama mamba a kwamitin gudanarwa na Federal Reserve.

Wannan naɗin ya samu yabo daga masu fafutikar kare ’yancin mata da ’yan tsiraru, waɗanda suka ce hakan ya nuna ci gaba a fannin da mata ba su da yawa.

Sai dai tun bayan dawowar Trump kan mulki, gwamnar ta fuskanci matsin lamba daga sabuwar gwamnatin, wacce ke sukar manufofin Babban Bankin musamman kan hauhawar farashin kaya da matsalar gidaje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments