Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan cewa, gwamnatinsa ta cimma yarjeniya da kasar Venezuela wanda ya bawa Amurka damar mallakar mafi yawan wuraren hakar man fetur na kasar Veneziueal wanda ya kai ganga biliyon 65.
Shafin labarai na yanar gizo Arab News ya nakalto Trump ya na cewa, wannan shi ne safaka na man fetur mafi girma wanda Amurka ta taba yi a tsawon tarihinta da wata kasa. Yace wannan safakar zai samar da kudade kimani dalar Amurka billiyon 100 ga kasar Venezuela.
Kasar Venezuela dai tana da ga cikin kasashen da suka fi ko wace kasa yawan man fetur a duniya. Gwamnatin kasar Venezuela dai ta shiga cikin karkashin ikon gwamnatin Amurka ne tun bayan da Trump ya tumbuke shugaba Nicolas madoro a farkon wannan shekarar.
Washington ta bar mataimakinsa Delcy Rodriguez ta ci gaba da mulkin matukar zata ci gaba da mulkin kasar bisa yanda Amurka take bukata.
Trump bai boye bukatarsa na kwace dimbin arzikin man fetur wanda kasar Venezuela take da shi ba, kuma a lokacinda ya bada sanarwan a shafinsa na yanar gizo ya ce, abinda suka samu a Venezuela ya ninka abinda Amurka take da shi na man fetur har sau biyu.