Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan rufe zirga zirgan jiragen sama kwata-kwata a kan sararin samaniyar kasar Venezuel daga yau, a cikin shirinsa na fara mamayar kasar.
Tashar talabijan ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto Trump yana fadar haka a shafinsa na sadarwa True Social. Ya kuma bayyana cewa wannan sako ne ga dukkan kamfanonin jiragen sama da matuka jiragen sama.
Trump ya aika da wannan sakon ne bayanda kasashen Espaniya da Potigal suka bukaci dukkan kamfanonin jiragen sama na kasar da su daina wucewa ta sararin samaniyar kasar Venezuela.
Shugaban ya kara da cewa, sojojinsa a shirye suke su shiga farautar masu safarar miyagun kwayoyi a kasar ta Venezuela, a aikin sojojin kasa a cikin yan kwanaki masu zuwa.
A cikin watan satumban da ya gabata jiragen yakin Amurka sun bude wuta kan kwale-kwale sun fi 10 a tashoshin jiragen ruwa na Venezuela inda mutane kimani 80 suka rasa rayukansu.