Shugaban kasar Amurka Donald Ttump ya ce, abu ne mai yiyuwa kasarsa ta sake kai wa wasu kasashen hari, don haka ba Venezuela ce ta karshe ba.
Shugaban kasar ta Amurka wanda ya yi hira da mujallar “The Atlantic” ta kasar Amurka ta wayar tarho a jiya Lahadi, ya bayyana cewa; Idan shugabar kasar Venezuela ta yanzu ba ta yi abinda ya dace ba, za ta dandanta kudarta, watakila fiye da Maduro.”
Haka nan kuma ya yi watsi da ra’ayinsa da siyasa da akan shi ne aka zabe shi, da shi ne kaucewa shiga yaki da sauya gwamnatocin kasashe,yana mai cewa, sauya gwamnati a kasar Venezuela ya fi halin da kasar ta kasance a baya.
Akan kasashen da za su iya fuskantar harin na Amurka, Donald Trump ya ce; Tabbas muna da bukatuwa da yankin Greenland, wanda a halin yanzu jiragen Rasha da China suke zagaye da shi.
A yau Litinin kuma shugaban kasar ta Amurka wanda ya yi Magana da ‘yan jarida a cikin jirgin sama, ya yi wa takwaransa na kasar Columbia barazana da cewa ba zai dade sosai akan karagar Mulki ba.
Shugaban kasar ta Amurka ya bayyana shugaban kasar Columbia Gustavo Petro da cewa maras lafiya ne, sannan kuma ya zarge shi da cewa yana da kamfani sarrafa tabar iblis (Cocaine).
Ita ma kasar Mexico ta shiga sahun kasashen da Donal Trump ya sake yi wa barazana a yau Litinin yana mai cewa, ta dawo cikin hayyacinta, kuma ‘ ya zama wajibi mu yi wani abu akan Mexico”.