Telegraph: Amurka Ta Taimaka Wa Wadanda Su Ka Kifar Da Basshar Asad

Jaridar Telegraph ta Birtaniya ta bayyana cewa, masu dauke da makamai da su ka kifar da gwamnatin  Syria, sun sami bayani daga Amurka da Birtaniya

Jaridar Telegraph ta Birtaniya ta bayyana cewa, masu dauke da makamai da su ka kifar da gwamnatin  Syria, sun sami bayani daga Amurka da Birtaniya akan cewa a wannan karon za a kifar da gwamnatin Basshar Asad.

A wata ganawa da aka yi a tsakanin runduna ta musamman ta Amurka da masu dauke da makaman, Amurka da Birtaniya su ka ba su horo, an bayyana musu cewa wannan shi ne lokacinku.

Bugu da kari, Amurkan ta sanar da rundunar nan ta “ Magawirus-saura” rundunar zaratan juyi, cewa su kara yawan adadin mayakansu domin a wannan karon ana shirin kifar da gwamnatin Basshar Asad.

Jaridar ta Telegraph ta ambato daya daga cikin kwamandojin wannan rundunar mai suna; Basshar Mashhadani yana cewa; An fada mana cewa; Ana gab da samun gaggarumin sauyi, wannan shi ne lokacinku na tarihi. Ko dai ku kifar da Basshar Asad, kuma ku ku fadi.”

Mashhadani ya kuma ce; Sai dai ba su bayyana mana wane lokaci hakan za ta faru ba, abinda su ka fada mana shi ne ku kasance cikin shiri.”

Har ila yau Mashhadani ya ce sun kara adadin mayakansu daga 800 zuwa 3000, kuma sun rike makamai na zamani, sannan kuma kowane mayakai ana ba su albashin dala 400.

Wani abu da jaridar ta yi ishara da shi, shi ne cewa adaidai lokacin da masu dauke da makamai su ka nufi birnin Damascus, ita kuwa wannan rundunar ta Magawirus-saura’ ta fita wajen garin “Tanaf” saboda hana ‘yan Da’esh’ motsawa,kamar yadda wani babban jami’in sojan Amurka ya bayyana.

Jaridar ta Birtaniya ta yi mamakin yadda Amurka ta yi aiki da kungiyar “Jabhatu-Tahrir-Sham’ wacce har zuwa 2017 tana tare da al’ka’ida.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments