Tel Aviv: Gagarumar zanga-zangar adawa da Netanyahu kan yakin Gaza

Dubun-dubatar yahudawa sun gudanar da gagarumar zanga-zangar nuna adawa da Shirin Netanyahu na ci gaba da kara fadada yakin da yake yi a Gaza. Masu

Dubun-dubatar yahudawa sun gudanar da gagarumar zanga-zangar nuna adawa da Shirin Netanyahu na ci gaba da kara fadada yakin da yake yi a Gaza.

Masu shirya zanga-zangar sun bayyana cewa, kusan rabin miliyan na Isra’ilawa ne suka gudanar da zanga-zanga a dandalin Hostages na Tel Aviv a daren jiya, inda kusan miliyan daya suka halarci zanga-zangar a sassan yankunan Falastinawa da Isra’ila ta mamaye, inda suka yi Allah wadai da yadda gwamnatin Netanyahu ke tafiyar da yakin Gaza.

Kungiyar masu neman a dauki matakan sako wadanda ake garkuwa da su ta bayyana taron na Tel Aviv a matsayin daya daga cikin mafi girma tun farkon yakin, tana mai cewa, “kusan mutane 500,000 ne suka taru…domin bayyana cewa, daukacin  Isra’ilawa na son a sako dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su a kawo karshen yakin.”

Amma duk da haka, firaminista Benjamin Netanyahu yana ci gaba da tsawaita yakin Gaza da gangan, wanda tuni ya kashe dubun-dubatar Falasdinawa, domin tsira a siyasance, ko da kuwa hakan zai kai ga kashe Isra’ilawa da ake tsare da su.

Da suke magana a gaban  dubban daruruwan mutane a Tel Aviv, iyalan wadanda aka kama sun zargi majalisar ministocin Netanyahu da yin watsi da ‘yan uwansu don ci gaba da yakin.

Ofir Braslavaski, mahaifin Rom Braslavski, ya ce ya ji ba shi da ƙarfi yayin da lafiyar ɗansa take tabarbarewa a lokacin da ya  bayyana a cikin faifan bidiyo na baya-bayan nan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted