Tehran ta bayyana aniyarta na karfafa hadin gwiwar ‘yan sanda da Nijar

Iran ta bayyana aniyarta ta karfafa hadin guiwar ‘yan sanda da Nijar. Wanna bayanin ya fito ne a wani bangare na ziyarar da, Birgediya Janar

Iran ta bayyana aniyarta ta karfafa hadin guiwar ‘yan sanda da Nijar.

Wanna bayanin ya fito ne a wani bangare na ziyarar da, Birgediya Janar Ahmad-Reza Radan, babban kwamandan rundunar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kai ziyara a kasar Nijar a ran gadinsa a Afrika.

A ziyarar tasa ya gana da firaministan Nijar Ali Lamine Zeine, da ministan harkokin wajen kasar Bakary Yaou Sangaré, da ministan harkokin cikin gida Janar Mohammed Tomba, da shugaban ‘yan sandan Nijar Janar Omar Chiyani.

A yayin ganawar, M. Zein ya jaddada karfafa hadin gwiwar ‘yan sanda a tsakanin kasashen biyu inda ya ce: “A shirye muke mu yi amfani da gogewar da ‘yan sandan Jamhuriyar Musulunci ta Iran suke da ita a dukkan fannoni.”

A nasa bangaren Janar Radan ya bayyana aniyar Iran ta mika kwarewar aikin ‘yan sanda zuwa Nijar tare da bayyana fatan kasashen biyu za su iya fadada hadin gwiwarsu a dukkan fannoni da suka hada da yaki da ta’addanci da safarar muggan kwayoyi da manyan laifuka.

A yayin ganawarsa da Mista Sangare, babban jami’in na Iran ya jaddada saukaka hadin gwiwa wajen musayar bayanai tsakanin  kasashen biyu, da mika wadanda ake zargi ta hanyar Interpol.

Tunda farko dama bangarorin sun sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da fahimtar juna wacce Janar Radan na Iran da Janar Mohammed Tomba, ministan cikin gida na Nijar suka rattabawa hannu

Bangarorin biyu sun jaddada karfafa hadin gwiwar ‘yan sanda, da musayar bayanai da yaki da ta’addanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments