Putin ya ba da shawarar tattaunawa kai tsaye da Ukraine a Istanbul

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba da shawarar yin  tattaunawa “kai tsaye” ba tare da sharadi ba” tsakanin kasarsa da Ukraine a ranar 15 ga Mayu a Istanbul. A martanin da ya mayar, shugaban na Ukraine ya ce a shirye ya ke don tattaunawa kai tsaye, amma ya zama dole a tsagaita bude wuta […]

Tehran ta bayyana aniyarta na karfafa hadin gwiwar ‘yan sanda da Nijar

Iran ta bayyana aniyarta ta karfafa hadin guiwar ‘yan sanda da Nijar. Wanna bayanin ya fito ne a wani bangare na ziyarar da, Birgediya Janar Ahmad-Reza Radan, babban kwamandan rundunar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kai ziyara a kasar Nijar a ran gadinsa a Afrika. A ziyarar tasa ya gana da firaministan Nijar Ali […]

Borrell : Rabin bama-baman da aka jefa a Gaza sun fito ne daga Turai

Tsohon jami’in harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Josep Borrell ya yi kakkausar suka ga kungiyar kan rashin daukar mataki game da kisan kiyashin da gwamnatin Isra’ila ke yi a zirin Gaza yana mai cewa “rabin bama-baman da aka jefa a zirin Gaza ne muke kawowa.” Da yake jawabi bayan karbar lambar yabo ta Carlos V […]

Matan Falasdinawa A Gaza Suna Fama Da Yunwa Mai  Tsanani Da Kuma Hare-haren HKI

Falasdinawa mazauna yankunan Khan-Yunus dake kudancin zirin Gaza suna fama da matsananciyar yunuwa, a lokaci daya suna fuskantar hare-hare masu tsanani daga sojojin HKI. Mata mazauna yankin sun fi fuskantar matsaloli saboda kananan yaran da suke tare da su, alhali kuma an rushe gidajensu. A tsawon yakin kisan kiyashin da HKI take yi, matan da […]

Pakisatan Ta Kore Cewa Ta Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wutar Yaki

 Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta jadada cewa ko kadan sojojin kasar ba su keta tsagaita wutar yaki da Indiya ba.  A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen ta Pakistan ta fitar ta ce; kasar tana ci gaba da aiki da tsagaita wutar yaki wacce aka sanar da ita, kuma sojojin kasar sun kai […]

Putin  Na Rasha Ya Gana Da Shugabannin Afirka Akan Batun Tsaro

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya karbi bakuncin shugabannin kasashen Afirka da su ka hada na Zimbabwe da na Burkina Fasa, inda su ka tattaunawa hanyoyin karfafa alaka a tsakanin kasashen nasu. Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da na Burkina Faso Ibrahim Taraore sun isa birnin Moscow domin halartar bikin cika shekaru 80 da samun nasara […]

  Iran Ta Yi Maraba Da Tsayar Da Wutar Yaki A Tsakanin Indiya Da Pakistan

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Tsagaita wutar yakin da aka yi a tsakanin Indiya da Pakistan abin yin maraba da shi ne, sannan kuma ya kara da cewa; Ya zama wajibi kasashen biyu su yi amfani da wannan dama domin rage tashin hankali a yankin da […]

An Yi Bikin Haihuwar Tauraro Na 8 Daga Taurari 12 Wasiyyan Manzon Allah(s)

Miliyoyin mutane, mafi yawansu mabiya mazhabar iyalan gidan manzon All..(s) sun taru a hubbaren limami na 8 daga limamai masu tsarki wasiyan manzon All..(s)..12. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, miliyoyin mutanen kasar Iran da kuma wasu bakin da suka zo daga kasashen waje sun yi cincirindo a hubbaren Imam Aliyu […]

Iran Ta Bayyana Damuwarsa Da Makaman Nukliyar HKI A Sanda Ake Takura Mata

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana fuska biyu na kasashen yamma, dangane da shirin magakamashin nukliya na kasarsa, da kuma yadda basa magana kan makaman nukliya wanda HKI take da su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Asabar, a birnin Doha na kasar […]