An bude taron manyan jami’an kungiyar hadin kan kasashen Asiya (ACD) a birnin Tehran na kasar Iran.
Taron wata dama ce ta tsakanin kasashe mambobin kungiyar na tattauna batutuwan da dama musamman wadanda suka fi daukan hankali a yankin ciki.
Mahalartar taron za kuma su tattauna batun Falasdinu da kuma Gaza.
An bude taron ne karkashin jagorancin mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin diflomasiya Mehdi Safari.
Manyan jami’ai daga kasashe 32 sun yi nazari kan sabbin abubuwan da suka faru a taron.
Ali Bagheri Kani, ministan harkokin wajen kasar Iran na riko, zai gabatar da jawabi a taron ministocin a hukumance yau litinin.
A cewar Mehdi Safari, tawagogi 41 da suka hada da ministocin harkokin waje, mataimakan ministocin harkokin wajen da babban sakatare na kungiyoyin Asiya ne suka halarci wannan taro.
Ana sa ran amincewa da sanarwar Tehran a karshen taron ministocin.