Tawagar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada cewa: Samar da mafita mai kyau a mashigar ruwan Hormuz ita ce kawo karshen yaki
Ofishin Jakadanci na Dindindin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya, ya mayar da martini ga daftarin kudirin da Amurka ta gabatar a Kwamitin Tsaron Majalisar, tana mai jaddada cewa: Mafita mai dorewa ga rikicin da ke faruwa a mashigar ruwan Hormuz ita ce dakatar da fadace-fadace na dindindin da kuma dage killace jiragen ruwan Iran.
Ofishin Jakadancin Iran ya bayyana a ranar Laraba cewa: Mafita mai amfani a mashigar ruwar Hormuz a bayyane take: kawo karshen yaki na dindindin, dage matakin killace jiragen ruwan Iran, da kuma dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa na yau da kullum.
Ofishin Jakadancin ya kara da cewa: “Akasin haka, Amurka tana tura daftarin kudiri mai dauke kuskure da bakar siyasa ga Kwamitin Tsaron Majalisar a karkashin hujjar ‘yancin jiragen ruwan kasashe na zirga-zirga a Mashigar, don ciyar da ajandar siyasa da kuma halatta ayyukanta haramtattu da suka saba dokoki, ba don nemo mafita ga rikicin da ke faruwa ba.”
Ofishin Jakadancin Iran ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana kira ga kasashe mambobin kwamitin Tsaron da su yi aiki bisa kwarewa, adalci, da ka’idoji, ba tare da tasirantuwa da matsin lamba ba, kuma yana kira gare su da su yi watsi da wannan daftarin kudiri kuma su guji goyon bayansa.