Tawagar dindindin ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasar za ta sa Isra’ila ta yi nadamar ta’addancin da ta aikata a baya-bayan nan kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran wanda ya kai ga shahadar babban jagoran Hamas Ismail Haniyeh.
Tawagar ta yi wannan furuci ne a ranar Laraba, yayin da take amsa tambayoyi kan zargin da ake yi wa kasar cewa za ta iya soke ramuwar gayya idan Tel Aviv ta cimma matsaya da kungiyar Hamas da za ta samar da zaman lafiya a yakin gwamnatin kasar ke yi a zirin Gaza.
“Mun bibiyar manyan al’amura guda biyu a lokaci guda,” in ji tawagar.
“Da farko dai, cimma daidaiton tsagaita wuta a Gaza da kuma janyewar ‘yan mamaya daga wannan yanki,” in ji tawagar ta Iran a MDD.
“Na biyu kuma, martani a kan kisan shahidi Haniyyah, da hana maimaita irin hakan. in ji tawagar.
Tun a ranar Larabar da ta gabata ne ministan harkokin wajen kasar Iran na riko Ali Bagheri Kani ya sake jaddada aniyar kasar na mayar da martani ga gwamnatin Isra’ila.
Kasar ba ta da wani zabi illa mayar da martani ga gwamnatin Isra’ila kan kisan gillar, in ji Bagheri, wanda ke jawabi a wani babban taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi. Na OIC.
Ya kuma kara da cewa, hakan ya zama wajibi domin dakile ci gaba da kai hare-hare kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, sakamakon rashin daukar mataki daga kwamitin sulhu na MDD.