Tawagar ECOWAS Ta Isa Guinea Bissau Don Magance Rikicin Siyasa A Kasar

Tawagar shugabannin kasashen Senegal da Salio, Bassirou Diomafaye da Juluis Maada Bio ta isa kasar Guinea Bissau a madadin kungiyar ECOWAS domin nemo mafita gameda

Tawagar shugabannin kasashen Senegal da Salio, Bassirou Diomafaye da Juluis Maada Bio ta isa kasar Guinea Bissau a madadin kungiyar ECOWAS domin nemo mafita gameda halin da aka shiga a kasar .

Ziyar tasu na zuwa kwanaki 45 da sojoji suka kwace mulki  bayan sun dakatar da babban zaben kasar da ake tsaka da yi kafin sanar da sakamakon zabe.

Ya zuwa yanzu babu wata sanarwa da aka fitar dangane da ziyarar, amma wata majiya ta ce tuni shugabannin kasashen suka gana da sojojin da ke kan mulki kafin su gana da bangaren ƴan adawa.

Babban burin da shugabanin kasashen na Senegal Bassirou Diomafaye  da takawanransa  na Salio Maa’ada Bio  ke san cimma wa shi ne samar da tabbaci game da wa’adin rikon kwarya akan mulki da sojojin ke son yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted