Tarayyar Turai: Idan Amurka Ta Kwace Greenland Kungiyar Nato  Za Ta Rushe

Kungiyar tarayyar turai ta yi gargadin cewa, matukar Amurka ta kwace iko da yankin Greenland da karfin soja, to karshen kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato ya zo. Jami’in kungiyar tarayyar turai mai kula da harkokin tsaro da kuma sararin samaniya Andrius Kubilius ya bayyana cewa; mamaye yankin na Greenland da Amurka za ta iya yi, […]

Amurka: Masu Adawa Da Siyasar Donald Trump Sun Yi Gangami A Birnin New York

Dubban masu adawa da siyasar Donald Trump na Amurka ne su ka yi gangami a kusa da “Central Park” dake birnin Newyork, sannan su ka nufi hasumiyar Trump dake cikin birnin. Dubban mutanen dai suna nun kin amincewarsu ne da kisan da wani jami’in ‘yan sanda ya yi wa wata mace wacce ‘yar hijira ce […]

Tawagar ECOWAS Ta Isa Guinea Bissau Don Magance Rikicin Siyasa A Kasar

Tawagar shugabannin kasashen Senegal da Salio, Bassirou Diomafaye da Juluis Maada Bio ta isa kasar Guinea Bissau a madadin kungiyar ECOWAS domin nemo mafita gameda halin da aka shiga a kasar . Ziyar tasu na zuwa kwanaki 45 da sojoji suka kwace mulki  bayan sun dakatar da babban zaben kasar da ake tsaka da yi […]

 Mutum Daya Ya Mutu Bayan Harin Da HKI Ta kai A Kudancin Labanon

Rahotanni daka birnin berut sun bayyana cewa sojojin HKI Sun kaddamar da wani hari a kudancin labanon a kuma yayi sanadiyar mutuwar wani mutum guda a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da HKI ke yi da aka rattaba hannu akai tun a shekara ta 2024. Ma’aikatar lafiya da  cibiyar bayar da […]

IRGC ta yi Allah wadai da tsoma bakin Trump a harkokin cikin gida na Iran

Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da tsoma bakin shugaban Amurka Donald Trump a harkokin cikin gida na kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar, IRGC ta jaddada cewa, kamar ayyukan tayar da zaune tsaye da makiya Iran suka yi a baya, laifukan tayar da zaune tsaye da […]

Shugaban Cuba : Mun shirya kare Cuba ‘har zuwa digon jini na karshe’

Shugaban Cuba Miguel Diaz-Canel ya yi watsi da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump kan kasarsa, yana mai jaddada cewa Havana a shirye take ta kare kanta “har zuwa digon jini na karshe.” Shugaba Diaz-Canel ya yi wannan tsokaci ne bayan da Trump ya yi ikirarin cewa babu wani karin mai ko kudi na Venezuela da […]

Gwamnatin Sudan ta koma Khartoum bayan shekaru biyu na yaki

Gwamnatin Sudan ta koma Khartoum babban birnin kasar a hukumance bayan fiye da shekaru biyu na yakin basasa da ya daidaita kasar.   Firaministan Sudan Kamel Idris ne ya sanar da hakan inda y ace gwamnatin kasar ta koma babban birnin inda zata maida hankali kan ayyukan inganta rayuwar jama’a. Wannan shi ne karon farko […]

Har yanzu Gaza na fuskantar hare-haren Isra’ila

Bayanai daga Gaza na cewa har yanzu Zirin na fuskantar hare-hare daga gwamnatin mamaya ta Isra’ila. Shaidu sun ba da rahoton cewa sojojin Isra’ila sun kai hare-hare ta sama, da kuma ruwan bama-bamai a yankuna da dama na Gaza, wanda hakan ke ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta wadda ta fara aiki tun daga […]