Tattaunawar Iran da Amurka na inganta zaman lafiya a yankin : Araghchi

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, tattaunawar dake tsakanin Iran da Amurka za ta iya taka rawar gani wajen samar da zaman

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, tattaunawar dake tsakanin Iran da Amurka za ta iya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

A yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen dandalin tattaunawa na Tehran, Araghchi ya ce kasashen yankin suna goyon bayan tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka.

” Zaman lafiya da kwanciyar hankali su ne batutuwa mafi muhimmanci ga dukkan kasashen yankin,” in ji shi.

Ya nanata matsayar Iran kan turbar diflomasiyya da kuma muhimmancin da take baiwa manufofin kyakkyawar makobtaka ta hanyar tattaunawa.

A wani bangare na jawabin nasa, ministan harkokin wajen na Iran ya ce dandalin tattaunawa na Tehran karo na shida ya samu halartar masana da jami’an kasashen waje da ba a taba ganin irinsa ba.

Wannan yunkuri a cewarsa, ya bayyana yuwuwar Teheran a matsayin cibiyar musayar ra’ayi kan batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da na ƙasa da ƙasa.

Bugu da kari, ministan harkokin wajen na Iran ya ce ya tattauna da takwarorinsa na Oman da Qatar kan tattaunawa da Amurka.

Mista Araghchi ya yi maraba da matakin da kasashen yankin musamman na yankin tekun Fasha suka dauka na sauya ra’ayinsu game da Iran, kamar yadda suke a matsayin “kyau” dangane da shawarwarin da aka yi tsakanin Tehran da Washington.

Idan dai ba a manta ba a farkon watan Afrilu ne aka fara tattaunawa tsakanin Iran da Amurka karkashin jagorancin masarautar Oman.

Ya zuwa yanzu dai an gudanar da shawarwari guda hudu kan shirin nukiliyar Teheran da kuma dage takunkumin. Bangarorin biyu duk sun bayyana tattaunawar a matsayin mai kyau da kuma amfani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments