Wani rahoto da Bankin Zuba Jari da Ci Gaba na kungiyar ECOWAS ya nuna cewa kasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar dake kawance a kungiyar Sahel sun samu ci gaban tattalin arziki mai kyau a 2025.
A cewar rahoton, Kasashen sun sami ci gaba da kashi 5.5% gaba daya, wanda hakan ya samo asali ne daga wadatar man fetur a Nijar da kuma farfaɗo da fannin hakar ma’adinai a Burkina Faso, in ji rahoton Sputnik Africa wanda ya ambato rahoton shekara-shekara na Bankin Zuba Jari da Ci Gaba na ECOWAS.
A cewar wannan rahoton, Nijar ta zama kasa mafi girma a Ƙungiyar a wannan bangaren, inda tattalin arzikinta ya karu da kashi 6.9% a 2025, wanda hakan ya sanya ta zama kasa ta uku mafi saurin bunkasa a tsakanin kasashe 15 na Yammacin Afirka.
Wannan ci gaban ya samo asali ne daga wadatuwar samar da mai, fitar da danyen mai, da kuma a bangaren bunkasar ayyukan noma.
A Burkna Faso kuwa Jimillar darajar kayayyakin cikin gida wato (GDP) ya karu da kashi 5.0% a shekarar 2025, wanda ya dan dara kashi 4.8% da aka samu a shekarar 2024.
Wannan ci gaban sakamako ne da ya samu ta hanyar ci gaba da fadada bangaren ayyukan samar da amfanin gona mai dorewa wanda ke amfana daga ruwan sama da shirye-shiryen tallafawa jama’a, da kuma farfado da masana’antar hakar ma’adinai a yayin da ake fuskantar hauhawar farashin zinare.
Tattalin arzikin Mali kuwa ya samu karuwar kashi 4.9% a shekarar 2025, kodayake wannan adadi ya dan yi kasa da kashi 5.0% da aka samu a shekarar 2024, wannan ya biyo bayan inganta samar da amfanin gona da kuma ci gaba da fadada bangaren ayyuka.