Tashar Jirgin Ruwa Ta “Eliat” Ta Kusa Durkushewa

Jaridar “Globes” ta HKI ta bayar da labarin dake cewa, a ranar Lahadi mai zuwa tashar jirgin ruwa ta “Eliat” za ta tsaya da aiki,

Jaridar “Globes” ta HKI ta bayar da labarin dake cewa, a ranar Lahadi mai zuwa tashar jirgin ruwa ta “Eliat” za ta tsaya da aiki, da dakatar da kai da komowar jiragen ruwa,bayan da aka rufe asusunsa saboda  basuka na kudin ruwa da su ka taru da sun wuce dala 162 a kowane wata.

Jaridar wacce ta tattalin arziki ce, ta ce an shiga cikin halin ko-ta-kwana akan batun, sannan kuma a hukumance an sanar da hukumar tashar jiragen ruwan halin da ake ciki na rufe asusun nasu saboda ba su biya kudin ruwan.

Har ila yau,an yi gargadin cewa daukar mataki irin wannan zai kai ga dakatar da ayyukan tashar jirgin ruwan ta hanyar hana shigowar jiragen ruwa masu dakon kaya.

Ita dai wannan tashar jiragen ruwa ta Eliat, tana a karkashin sarrafawar kamfanin “Naqash Ikhwan” da ‘yan kasuwa ne yahudawa a Amurka. An ba su hayar tafiyar da wurin ne dai na tsawon shekaru 15 a kan kudi dalar Amurma miliyan 32.4, za kuma a iya jaddada hayar a cikin duk shekaru 10.

Tashar jirgin ruwan dai tana daga cikin wuraren da Ansarullah na Yemen suke kai wa hare-hare da makamai masu linzami da kuma jiragen sama marasa matuki.

A ranar Talata din da ta gabata ma dai an harba wa tashar jiragen ruwa jirage marasa matuki guda uku daga Yemen. Sanarwar Ansarullah ta kunshi cewa, za su ci gaba da kai hare-hare har zuwa lokacin da za a kawo karshe yakin Yemen da kuma daukewa yankin takunkuman da aka kakaba masa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted