Iran, Pakistan, Saudiyya da Turkiyya sun tabbatar da ci gaba da tattaunawa kan zaman lafiya da tsaro a yankin
An fitar da wata sanarwa game da taron sassa huɗu tsakanin Iran, Pakistan, Turkiyya da Saudiyya kan tsaro da kwanciyar hankali na yankin. Sanarwar ta bayyana cewa mahalarta taron sun amince su ci gaba da tattaunawa da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe huɗu a yankin, ciki har da a fannin zaman lafiya da tsaro na yankin.
A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, sanarwar manema labarai ta bayyana cewa an gudanar da taron farko na ƙasashen yankuna huɗu a ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, a birnin Tehran fadar muilkin Iran.
Sanarwar ta ƙara da cewa Manjo Janar Mohsen Reza’i, Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya jagorancin zaman taron.
Sanarwar ta kuma lura da halartar Ministan Tsaron Saudiyya Khalid bin Salman, Shugaban Sojojin Pakistan Asim Munir, da Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya Ibrahim Kalin.
Sanarwar ta kammala da jaddada cewa mahalarta taron sun amince su ci gaba da tattaunawa da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen yankuna huɗu, ciki har da a fannin zaman lafiya da tsaro na yankin.