Tarayyar Turai: Muna Goyon Bayan Warware Batun Nukiliyar Iran Ta Hanyar Diplomasiyya

Jami’ar siyasar waje ta tarayyar turai Kaja Kallas ta bayyana cikakken goyon baya ga warware batun makamashin Nukiliyar Iran ta hanyar diplomasiyya. Jami’ar ta wallafa

Jami’ar siyasar waje ta tarayyar turai Kaja Kallas ta bayyana cikakken goyon baya ga warware batun makamashin Nukiliyar Iran ta hanyar diplomasiyya.

Jami’ar ta wallafa a shafinta na X cewa: Na tattauna da ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci domin tabbatar da goyon bayan kungiyar tarayyar turai akan aiki da hanyar diplomasiyya domin warware batun Nukiliyar Iran da kuma rage rikice-rikice a cikin wannan yankin.”

Haka nan kuma Kallas ta jaddada abinda a baya tarayyar turai din ta rika riyawa da ba shi da tushe na cewa, Iran tana bai wa Rasha taimakon soja tana mai cewa: ” Na kuma yi kira ga Iran da ta dakatar da bai wa Rasha taimakon soja.”

Iran dai ta sha yin watsi da wannan irin zargin na cewa tana bai wa kasr Rasha makamai.

Matsayar tarayyar turai din dai ta zo ne bayan yin zango na uku na tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka ta hanyar shiga tsakanin kasar Oman wacce aka fara tun a karshen watan Afrilu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments