Sharhin bayan Labarai: Ci Gaban Harkokin Kasuwanci Tsakanin Iran Da Kasashen Waje Duk Tare Da Takunkuman Kasashen Yamma

Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da “Bankasar tattalin arzikin Iran duk tare da takunkuman tattalin arziki masu tsanani wadanda kasashen yamma musamman Amurka suka doramata, wanda ni tahir amin zan karanta. ////…A dai-dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka take barazanar zata hana sayan danyen man fetur daga kasar Iran kwatakwata, […]

 Sojojin HKI Sun Kai Hare-hare A Sassa Mabanbanta Na Kasar Yemen

Tashar talabijin din HKI ta channel: 12 ta nakalato sojoji suna sanar da kai wa Yemen hare-hare. Sanarwar ta kuma ce; jiragen yakin HKI sun kai hare-hare ne a wurare 9 a lokuta daban-daban da su ka hada da tashar jiragen ruwa ta Hudaidah. Sojojin na HKI sun ce jirage 30 ne su ka kai […]

Tarayyar Turai: Muna Goyon Bayan Warware Batun Nukiliyar Iran Ta Hanyar Diplomasiyya

Jami’ar siyasar waje ta tarayyar turai Kaja Kallas ta bayyana cikakken goyon baya ga warware batun makamashin Nukiliyar Iran ta hanyar diplomasiyya. Jami’ar ta wallafa a shafinta na X cewa: Na tattauna da ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci domin tabbatar da goyon bayan kungiyar tarayyar turai akan aiki da hanyar diplomasiyya domin warware batun […]

Iran Ta Mayar Da Martani Akan Zarginta Dangane Da Yemen

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi watsi da zarge-zargen da aka yi ma ta dangane da kasar Yemen.  A wani bayani da ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran din ta fitar ta bayyana cewa: Abinda mutanen Yemen suke yi domin taimakawa al’ummar Falasdinu, mataki ne na kashin kansu da su ka dauka cikin ‘yanci […]

 Kotun Duniya Ta Wanke HDL Akan Zargin Kisan Kiyashi A Sudan

Kotun duniya ta yi watsi da karar da Sudan ta kai Hadaddiyar Daular Larabawa tana mai zarginta da hannu a kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar wannan kasa. A yau Litinin ne kotun duniyar ta yi watsi da karar ta Sudan, tana mai wanke Hadaddiyar Daular Larabawa. Ita dai Sudan ta zargi Hadaddiyar Daular […]

Amurka sake kai sabon hari kan kasar Yemen

Amurka na kara kai hare-hare ta sama a yankuna daban-daban na kasar Yemen. Babban birnin kasar, Sanaa, shi ne Amurka ta kai wa hari a safiyar yau Litinin. Wasu hare-hare ta sama da Amurka ta kai a yankunan Bani Matar, Bani Hushaysh da Bani Al-Harith a birnin Sanaa. Hakazalika, harin da jiragen yakin Amurka suka […]

Iran da Saudiyya sun jaddada bukatar kare hurimin kasar Siriya

Kasashen Iran da kuma Saudiyya sun jaddada kiran su na ganin an kare hurumin kasar Siriya tare kuma da yin tir da hare-haren da Isra’ila ke kai wa kasar. Jami’an Iran da Saudiyya sun tabbatar da aniyarsu ta tabbatar da ‘yancin kai da kuma ‘yancin yankin Siriya, tare da yin Allah wadai da harin da […]

Yau Kotun ICJ ke yanke hukunci kan zargin da Khartoum ke wa UEA

Yau Litinin ne kotun kasa da kasa ta ICJ za ta yanke hukunci kan karar da Sudan ta shigar kan Hadaddiyar Daular Larabawa. Khartoum ta kai karar UAE a gaban kotun kasa da kasa da ke birnin Hague, inda ta zarge ta da hannu wajen kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar Masalit, sakamakon zarginta […]