Tarayyar Afirka ta yi Allah wadai da juyin mulkin a Guinea-Bissau

Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Mahmoud Ali Youssouf, ya yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Guinea-Bissau a ranar Alhamis, inda ya

Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Mahmoud Ali Youssouf, ya yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Guinea-Bissau a ranar Alhamis, inda ya yi kira da a gaggauta sakin hambararren shugaban kasar Umaro Sissoco Embaló da sauran jami’an da ake tsare da su.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta sake nanata cewa kungiyar Tarayyar Afirka ba za ta amince da duk wani sauyi na gwamnati da ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar ba.

Ya jaddada muhimmancin mutunta tsarin zabe da ake gudanarwa da kuma tabbatar da tsarin mulkin kasar, kamar yadda hukumar zabe ta kasar ta tanada.

Youssouf ya yi kira ga dukkan bangarorin da su yi taka tsantsan don hana ci gaba da tabarbarewar lamarin, yana mai jaddada shirin kungiyar na yin aiki kafada da kafada da ECOWAS da abokan huldar kasa da kasa don maido da kwanciyar hankali da kiyaye tsarin dimokuradiyya a Guinea-Bissau.

Tarayyar Afirka ta tabbatar da goyon baya da hadin kai ga al’ummar Guinea-Bissau kan hanyar samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da tabbatar da mulkin dimokuradiyya.

Kasashe da kungiyoyi da hukumomi da dama sun yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a kasar Guinea Bissau da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya, da Portugal, da Ghana, da Najeriya, da shugabannin hukumar zabe da dai sauransu, inda suka yi kira da a gaggauta maido da tsarin mulkin kasar Guinea-Bissau, mutunta tsarin dimokuradiyya da warware duk wasu korafe-korafe na zabe ta hanyar lumana, gaskiya, kuma bin doka da oda.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments