Tanzania: ‘Yan sanda sun kama wani babban jigon adawar siyasa

‘Yan sandan Tanzania sun kama Amani Gologowa, mataimakin sakatare janar na jam’iyyar adawa ta Chadema a ranar jiya Asabar, bayan zanga-zangar da ta barke bayan

‘Yan sandan Tanzania sun kama Amani Gologowa, mataimakin sakatare janar na jam’iyyar adawa ta Chadema a ranar jiya Asabar, bayan zanga-zangar da ta barke bayan zaben makon da ya gabata.

Hukumomi sun sanar da sunayen wasu mutane 9 da ake nema ruwa a jallo dangane da abubuwan da suka faru. Jam’iyyar Chadema da wasu mambobi na kungiyoyi masu fafutukar kare hakkin dan adam da dama sun yi ikirarin cewa, jami’an tsaro sun kashe mutane sama da 1,000 yayin da suke tarwatsa zanga-zangar, alkaluman da gwamnati ta yi watsi da su a matsayin marasa tushe, amma kuma gwamnatin ba ta bayar da adadin wadanda suka mutu a hukumance ba.

‘Yan sanda sun sanya Gologowa da wasu mutane tara a cikin jerin sunayen da ake nema ruwa a jallo a matsayin wani bangare na bincikensu kan rikicin, kwana guda bayan da masu gabatar da kara suka tuhumi mutane 145 da laifin cin amanar kasa dangane da abubuwan da suka faru kwanan nan bayan sanar da sakamakon zaben da aka yi takaddama a kan sakamakonsa.

Chadema ita ce babbar jam’iyyar adawa a Tanzania kuma ta yi ikirarin cewa sakamakon zaben da aka fitar ya kasance cike da rashin tsari da keta doka, yayin da gwamnati ta dage a kan cewa tsarin zaben ya gudana cikin yanayi mai tsafta  kuma karkashin cikakkiyar kulawar bangaren shari’a.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments