Taliban Tace Hare Haren Pakistan Sun Kashe Mutane 9

Gwamnatin Taliban ta kasar Pakistan ta bada sanarwan cewa mutane 9 ne fararen hula suka rasa rayukansu sanadiyyar hare haren jiragen yaki na kasar Pakistan

Gwamnatin Taliban ta kasar Pakistan ta bada sanarwan cewa mutane 9 ne fararen hula suka rasa rayukansu sanadiyyar hare haren jiragen yaki na kasar Pakistan a lardun Kunar da kuma Helmand.

Amma majiyar gwamnatin kasar Pakistan ta bayyana cewa ta kasi hare hare a larduna biyu ne, kuma ta kashe yan ta’adda ne 22. Bata kashe fararen hula ba.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin gwamnatin Yaliban Zabihullah Mujahid yana fada a shafinsa na X kan cewa, mutanen da aka kashe mata da yara ne, kuma sun rusa gidaje guda 3.

Mujahid yayi tir da hare haren na Pakistan ya kuma kara da cewa gwamnatin Afganistan bata goyon bayan kungiyoyin yan ta’adda kamar yanda Pakistan take riyawa.

Amma ofishin MDD a kasar Afganistan ya bada sanarwan cewa ya lissafa mutane 1,100 fararen hulan da aka kashe a hare hare tsakanin kasashen biyu makobta acikin wannan shekara ta 2026 kadai.

Afganistan ta bayyana cewa matsalar kan iyakar kasashen biyu matsalar cikin gida ne, kungiyar TTP ta mutanen Pakistan ne wadanda suke boyewa a cikin tsaunukan Afganistan don ayyukan ta’addancin a cikin Pakistan. Tace bata da alaka da su. Amma Pakistan tace Afganistan na taimakamasu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted