Wani babban jami’in ‘yan sanda a jihar Uttar Pradesh ta Indiya ya bukaci musulmi da su yi sallar Juma’a a gida.
A cewar radiyon gwamnatin Pakistan, Firimiyan Jihar Uttar Pradesh Yogi Adityanath ya kare kalaman jami’in ‘yan sandan game da musulmi, inda ya ce, “A yayin da ake gudanar da bukukuwan Holi sau daya a shekara, ana gudanar da sallar Juma’a a duk mako.”
Ya bayyana jami’in a matsayin gwarzo jarumi, tare da bayyana cewa wannan ra’ayi nasa daidai ko da kuwa hakan ya bakantawa wasu.
Ya kara da cewa: “Bikin Holi ya fi sallar Juma’a muhimmanci, amma ana gudanar da shi sau daya ne kawai a shekara, don haka gudanar da shi yana da fifiko a kan Jum’a.”
Jami’in ‘yan sandan da ake magana a kai ya fada a wata hira da manema labarai cewa: “Idan musulmi suna son fita to babu matsala, kuma idan aka watsa musu musu kaloli to kada su yi korafi kan hakan, ko kuma su zauna a gida.
Firimiyan Uttar Pradesh ya bayar da hujjar cewa ana iya jinkirta Sallar Juma’a har zuwa lokacin da ‘yan Hindus za su kammala bukukuwansu, ko kuma kowane musulmi ya yi sallar Juma’a a gida.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da malamin addinin musulinci Maulana Khalid Rashid Faranji ya bayyana cewa za a gudanar da sallar Juma’a kamar yadda aka saba a ranar 14 ga watan Maris, ranar da ‘yan addinin Hindus suke gudanar da wasu bukukuwansu na addini.