Takunkuman MDD kan Iran sun fara aiki

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sake kakabawa Iran  takunkumman da aka dage wa kasar a karkashin yarjejeniyar nukiliyar ta shekarar 2015, matakin da

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sake kakabawa Iran  takunkumman da aka dage wa kasar a karkashin yarjejeniyar nukiliyar ta shekarar 2015, matakin da ya biyo bayan zargin da kasashen Turai ke yi kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.

Kwamitin sulhun ya maido da takunkumin ne a cikin daren jiya, wanda ya hada da toshe kadarorin Iran da ke ketare, da dakatar da kwangilar sayen makamai da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da kuma makamai masu linzami na kasar.

Wannan shawarar dai na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan da Amurka da kawayenta suka yi watsi da daftarin kudurin da kasashen Sin da Rasha suka gabatar, na neman jinkirta matakin dawo da takunkuman.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted