Ana ci gaba da takun saka tsakanin Rasha da Faransa biyo bayan kalaman Emmanuel Macron na baya-bayan nan game da kayyade makaman nukiliya.
Moscow ta dauki wadannan kalamai a matsayin barazana kai tsaye, yayin da Paris ke kare matsayinta ta hanyar jaddada bukatar kare Turai, Wanda ya nuna yadda ake samun rashin jituwa sosai kan batun Ukraine.
Moscow ta yi imanin cewa Emmanuel Macron, wanda ya yi Allah wadai da “tashin hankali” na Rasha yayin jawabinsa a yammacin Laraba, yana son “yakin (a Ukraine) ya ci gaba.”
Ministan harkokin wajen Rasha ya yi la’akari da cewa kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron, wanda ya nuna yuwuwar kariyar Turai da laima ta nukiliya “barazana” ce ga Rasha.
A sa’i daya kuma, Sergei Lavrov ya yi watsi da duk wata yuwuwar yarjejeniya da Moscow kan batun tura dakarun wanzar da zaman lafiya na Turai a Ukraine domin tabbatar da tsagaita bude wuta.