Syria Ta Yi Watsi Da Zargin Janyewar Sojojinta Daga Birnin Hama

Syria ta yi watsi da zargin janyewar sojojinta daga birnin Hama da ke arewacin kasar, a tunkarar ‘yan ta’addar da ke samun goyon bayan kasashen

Syria ta yi watsi da zargin janyewar sojojinta daga birnin Hama da ke arewacin kasar, a tunkarar ‘yan ta’addar da ke samun goyon bayan kasashen waje.

A wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar tsaron kasar ta Syria ta ce an jibge sojojin a yankunan arewaci da gabashin birnin, tana mai cewa, “Ba a shiga garuruwan da ke kusa da Hama ba.”

Don haka, ta bukaci ‘yan kasar da “kar su yarda da jita-jita da kafafen yada labarai na ‘yan adawa suka fitar.”

Sanarwar ta ce sojojin sun sake tura sojoji zuwa yankuna da dama na arewacin kasar a shirye-shiryen tunkarar harin da ‘yan ta’addan.

Bayan haka, an kuma bayar da rahoton cewa, sojojin Syria sun dakile manyan hare-haren ta’addanci a lardin Aleppo, ta hanyar wani farmaki na karya laggon ‘yan ta’addan.

Babban kwamandan rundunar ya ambato cibiyar hadin gwiwa ta Rasha da ke kasar Syria na cewa sojojin kasar da kawayenta na sojojin sama na Rasha sun kashe ‘yan ta’adda kusan 300 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata bayan kawar da 600 daga cikinsu a cikin kwanaki biyun da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments