Syria:  Mutanen Da Aka Kashe A cikin Shekara Daya Sun Kai  1348

Kungiyar kare hakkin bil’amada ta kasa Syria “almarsad” ta ce, a cikin shekarar nan ta 2025 mai karewa, adadin mutanen da aka kashe a kasar

Kungiyar kare hakkin bil’amada ta kasa Syria “almarsad” ta ce, a cikin shekarar nan ta 2025 mai karewa, adadin mutanen da aka kashe a kasar sun kai 1348, kuma rabinsu akan bangaranci ne.

Kungiyar ta ce; an yi wannan kisan ne daga ranar 8 ga watan Disamba 2024 zuwa wannan watan na Disamba 2025, daga cikin mutanen da     akwai 575 da an kashe su ne saboda bangaranci ne.

Wani sashe na rahoton ya kuma ce kasashen da aka yi, sun faru a cikin mafi yawancin biranen kasar, saboda rashin bayar da kariya ga fararen hula.

Kungiyar kare hakkin bil’adaman ta kuma bayyana cewa, kisan da ake yi yana a matsayin wata karaurawar hatsari ne akan yadda al’ummar kasar take kama hanyar durkushewa.

Biranen da kashe-kashen su ka yawaita, sun hada da Hama, Hums,Lazikiyya da Tartus.

A cikin wannan shekarar ta 2025 kuwa an sami karuwar kashe-kashen zuwa 194, daga cikinsu da akwai kananan yara da mata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted