Araghchi ya soki kasashen E3 game da matakinsu kan shirin nukiliyar Iran  

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya soki kasashen nan guda uku na turai game da matakinsu na baya baya nan a game da shirin nukiliyar Iran. A wata tattaunawa ta wayar tarho da ta yi da takwararsa ta Birtaniya Yvette Cooper, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya jaddada sha’awar Jamhuriyar Musulunci ta Iran […]

Rasha na taro da ministocin Afrika a Masar

Kasar Rasha na wani babban taronta da abokan huldarta na Afirka a kasar Masar da nufin inganta dangantakar tattalin arziki da fadada tasirinta a Afirka. Taron na zuwa ne a daidai lokacin da kawayen Ukraine ke kokarin maida Rasha saniyar ware ta fuskar diflomasiyya. A karon farko dai, ana gudanar da wannan taron a nahiyar […]

Iran : An zartar da hukuncin kisa kan wani dan leken asirin Isra’ila

A Iran an zartar da hukuncin kisa kan wani dan kasar dake liken asiri wa gwamnatin Isra’ila. Ma’aikatar shari’a Ta ke an zartar da hukuncin kisan ne kan Aqil Keshavarz, bias samunsa da laifin leken asiri da hadin gwiwa da Isra’ila, bayan Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin kisa a kansa. An kama shi a […]

CAF : Za a rika yin gasar AFCON duk bayan shekaru hudu, daga 2028

Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta sanar da cewa nan ba da jimawa ba za a rika gudanar da gasar cin kofin Afirka bayan shekaru hudu, maimakon bayan shekaru biyu. Hukumar ta sanar da hakan ne, a Rabat, babban birnin kasar Morocco a jajibirin wasan farko na gasar cin kofin Afirka (AFCON). Wannan babban […]

Mali na karbar Taron koli na biyu na Hadakar Kasashen Sahel (AES)

An bude taron koli na Hadakar kasashen Sahel, a wannan Asabar a Bamako babban birnin kasar Mali. Taron zai hada shugabannin kasashen Mali, Nijar, da Burkina Faso a ranakun 22 da 23 ga Disamba. Tun da farko dai an fara da zaman “Majalisar Ministocin kungiyar wanda ya hada ministocin da ke kula da harkokin kasashen […]

 Kasar Moroko Ta Lashe Kofin Kasashen Larabawa

Kungiyar kwallon kafa ta Moroko ta lashe kofin kasashen larabawa bayan da ta buga da kasar Jordan, a kasar Qatar a ranar Alhamis. A can birnin Rabat babban birnin kasar ta Moroko masu sha’awar kwallon kafa sun fito kan tituna domin nuna murna akan nasarar da kasar tasu ta samu na lashe kofin kasashen larabawan. […]

Syria:  Mutanen Da Aka Kashe A cikin Shekara Daya Sun Kai  1348

Kungiyar kare hakkin bil’amada ta kasa Syria “almarsad” ta ce, a cikin shekarar nan ta 2025 mai karewa, adadin mutanen da aka kashe a kasar sun kai 1348, kuma rabinsu akan bangaranci ne. Kungiyar ta ce; an yi wannan kisan ne daga ranar 8 ga watan Disamba 2024 zuwa wannan watan na Disamba 2025, daga […]

Rasha Ta Kira Yi Hukumar ( IAEA ) Da Ta Zama ‘Yar Ba-Ruwanmu Akan Batun Iran

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya ce; Moscow ta bukaci ganin shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta duniya Refael Grossy ya zama dan baruwanmu akan batun makamashin Nukiliya na Iran, ya yi amfani da kwarewa a cikin aikinsa. Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto Lavrov da ya gabatar da taron manema labaru a jiya […]

MDD: Rudnunar RSF Ta Kashe Mutane 1,000 A Sansanin ‘Yan Hijiara Na Zamzam

MDD

Wani rahoto da MDD ta fitar a ranar Alhamis din da ta gabata ya kunshi cewa, rundunar kai daukin gaggawa, ( RSF) ta kashe fararen hula 1,000 a sansanin ‘yan hajara na Zamzam dake yankin Darfur a cikin watan Aprilu na wannan shekarar ta 2025. Rahoton dai yana a matsayin wani sabon zargi ne ga […]

Putin: Tsagaita Wuta A Ukraina Yana Hannun Kasashen Yamma Da Kiev

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa dakatar da budewa juna wuta a yakin Ukraine a halin yanzu yana hannun kasashen yamma da kuma ita Ukraine. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban Putin yana fadar haka a jiya Jumma’a a jawabin karshen shekara da ya gabatar a birnin Mosco. Ya […]

Amurka Ka Kai Hare-Haren Daukar Fansa Kan ISIS A Kasar Siriya

Gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa ta kai hare-hare ta sama da kasa a wasu yankuna a kasar Siriya don halaka mayakan ISIS wadanda take zargi da kashe sojojin Amurka biyu a yankin Palmyra na tsakiyar kasar ta Siriya. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yaki na kasar Amurka Pete […]

Morocco Da Lashe Kofin Gasar Kwallon Kafa Ta Kasashen Larabawa

Yan wasan kwallon kafa na kasar Morocco sun lashe gasar kwallon kafa ta kasashen Larabawa a wani wasan da suka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar tare da kasar Jordan. Shafin yanar gizo nalabarai Africa News ya bayyana cewa masu goyon bayan kungiyar kwallon kafar ta Morocco a birnin Rabat sun cika tituna suna […]