An sami hatsarin tashin gobara a cikin wani rumbun ajiyar makamai a garin Mu’arrah dake gundumar Idlib ta Arewa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar mutane da dama.
Majiyar kiwon lafiya ta kasar Syria ta bayyana cewa; Mutane 2 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 70 su ka jikkata sanadiyyar fashewar rumbun makamai a garin Mu’arrah Masrin.
Hukumar agjin gaggawa ta kasar Syria ta ce; Har yanzu babu cikakken dalili akan abinda ya haddasa wannan gobarar ta Mu’arrah Msarin.
Ma’aikatan kwana-kwana sun nufi wurin da gobarar ta tashi domin kashe wuta da kuma dauke mutanen da su ka jikkata.