Syria: Mutane Da Dama Sun Mutu Da Kuma Jikkata Sanadiyyar Gobara A Rumbun Ajiyar Makamai

An sami hatsarin tashin gobara a cikin wani rumbun ajiyar makamai a garin Mu’arrah dake gundumar Idlib ta Arewa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar mutane da dama. Majiyar kiwon lafiya ta kasar Syria ta bayyana cewa; Mutane 2 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 70 su ka jikkata sanadiyyar fashewar rumbun makamai a […]
“Human Right Watch” Ta Yi Kira Da A Saki Tsohon Shugaban Nijar Muammad Bazoum

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Human Right Watch” ta yi kira ga gwamnatin sojan jamhuriyar Nijar da ta saki tsohon shugaban kasar Muhamad Bazum, wanda ake tsare da shi tun lokacin juyin mulkin watan Yuli na 2023. Kungiyar ta kuma ce, ci gaba da tsare Muhammad Bazum da ake yi ba tare da yi masa […]
An Jikkata Sojojin Sahayoniya 9 Ta Hanyar Take Su Da Mota

Kafafen watsa labarun HKI sun ce wani mutum a cikin motar da yake tukawa ya nufi kan ‘yan sahayoniya a mahadar “Hahsrun” a kusa da “Kafar-Yona”dake yammacin Tul-Karam. Bayan da matumin ya take ‘yan sahayoniyar ya fice daga yankin ba tare an iya tsayar da shi ba. Majiyar ta kara da cewa; 9 daga cikin […]
Iran: Iran Tana Cikin Kasashe Biyar Na Duniya Da Suka Ci Gaba Wajen Kiwon Dabbobi

Ministan Noma na Iran Gulam Riza Nuri Qazlajeh ya fada a yau Alhamis cewa; Iran tana a cikin kasahe biyar na sahun gaba da su ka yi fice wajen kiwon dabbobi. Minstan wanda yake jawabi a wani kamfani na samar da nono, ya ce, Iran tana da niyyar kara yawan dabbobin da suke samar da […]
Fiye Da Falasdinawa 111 Ne Su Ka Yi Shahada Saboda Yunwa A Gaza

Majiyar asibitocin yankin Gaza ta tabbatar da cewa, Falasdinawa 115 sun yi shahada sanadiyyar yunwa saboda karewar abinci a cikin yankin. Ita kuwa hukumar Agajin MDD dake aiki a Falasdinu “Unrwa” ta sanar da cewa tana da dubban manyan motoci da suke cike da kayan abinci suna jiran a ba su umaranin shiga Gaza.” Motocin […]
Ayatullahi Shirazi Ya Jinjinawa Al’ummar Iran Kan Hadin kansu A Lokacin Yakin Kwanaki 12

Ayatullah Makarem Shirazi ya jaddada cewa: An kara samun karfafan hadin kan al’umma Iran bayan wuce gona da irin ‘yan sahayoniyya da Amurka kan kasarsu Ayatullah Nasser Makarem Shirazi, babban malamin addinin Musulunci a birnin Qum mai tsarki na kasar Iran ya jaddada cewa: An kara samun hadin kan kasa bayan yakin wuce gona da […]
Kwamitin Tsaron MDD Ya Fara Tattaunawa kan Matsalolin Yankin Gaza

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara tattauna masifar da ta faru a Gaza tare da jaddada kawo karshen kisan kiyashi yanki Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani sabon zama domin tattauna batutuwan da suke faruwa a Gaza da kuma tabarbarewar al’amuran jin kai a yankin, inda ake ci gaba da yin […]
Asusun “UNICEF” Ya Yi Gargadi Kan Bala’in Jin Kai A Gaza

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi karuwar bala’i na jin kai a Gaza Kazem Abu Khalaf, kakakin hukumar UNICEF a Falasdinu, ya tabbatar da cewa: Abin da ke faruwa a Gaza ba a taba ganin irinsa ba, yana mai cewa har yanzu yana ci gaba da tuntubar wasu ma’aikatan […]
Majalisar Dokokin Isra’ila Ta Kada Kuri’ar Sake Mamaye Yankunan Flasdinawa

Gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da karya dokokin kasa da kasa, inda ta fara mamaye yankunan Gabar Yammacin Kogin Jordan da kwarin Jordan! Majalisar Dokokin yahudawan sahayoniyya ta Knesset ta kada kuri’a kan wani kudirin doka da ba shi da tushe don tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila cikakken ikon mallakar yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan […]
Gwamantin Siriya Ta Rufe Hanyoyin Shiga Birnin Suweida Saboda Ci Gaba Da Rikici

Hukumomin rikon kwaryar Siriya sun rufe hanyoyin zuwa birnin Sweida bayan sake bullar wani tashin hankali Dakarun gwamnatin Siriya na ci gaba da rufe hanyoyin da ke shiga lardin Sweida da ke kudancin kasar tun daga wayewar garin ranar Asabar, bayan kazamin fadan da aka gwabza tsakanin kabilar Bedouin da mayakan Duruz a cikin birnin. […]
Iran Tace Tawagar Kwararru Daga Hukumar IAEA Zata Ziyarci Kasar Nan Ba Da Dadewa Ba

Tawagar kwararru daga hukumar makamashin Nukliya IAEA zata ziyarci kasar Iran nan ba da dadewa ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Kazem Gharibabadi mataimakin ministan harkokin wajen kasar a bangaren sharia da kuma harkokin kasashen waje ne ya bayyana haka. Ya kuma kara da cewa tawagar zata tattauna da Jami’an gwamnatin […]
Yan Majalisar Dokokin Kasashen Iran Da Iraki Sun Amince Da Ra’yin Ficewar Sojojin Amurka Daga Iraki

Yan majalisar dokokin kasar Iran sun bukaci majalisar dokokin kasar Iraki su kori sojojin Amurka daga kasar ta Iraki. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran yana cewa, yan majalisar dokokin kasar Iran sun bayyana haka ne a lokacin ganawasu da wani dan majalisar dokokin kasar Iraki mai wakiltan lardin Karbalar Imam Hussain (a) a […]
Iran Ta Zargi Amurka Da Isra’ila Da Keta DokokiDa Yarjeniyoyin Kasa Da Kasa

Wani babban Jami’in diblomasiyyar kasar Iran ya zargi Amurka da kuam HKI da laifin Zagon kasa ga dokokin kasa da kasa da kuma sabawa yarjeniyoyi da dokokin MDD. Kazen Gharibabadi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan al-amuran sharia na kasa da kasa yana fadar haka a jiya Laraba a majalisar dinkin duniya a birnin […]
Brazil Ta Shiga Yaki Da HKI, Inda Ta Kudurin Anniyar Goyon bayan Afirka Ta Kudu A Kotun ICJ

Gwamnatin kasar Brazil tana shirin bayyana goyon bayanta ga Afirka ta kudu a karar da ta shigar a gaban kotun ICJ dangane da tuhumar jami’an gwamnatin HKI da aikaya kisan kiyashi a Gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wata jaridar kasar Brazil Folha De S tana fadar haka. Sannan kamfanin dillancin […]