Da marecen jiya Laraba jiragen yakin HKI sun kai wasu jerin hare-hare akan biranen Damascus, Hums, Dar’ada Humah.
Tashar Talabijin din ‘almayadin’ wai watsa shirye-shiryenta daga kasar Lebanon ta bayyana cewa; An kai harin ne akan wata cibiyar bincike a yankin Barzah dake arewacin birnin Damascus.
Wata majiyar asibiti ta shaida wa tashar talabijin din ta almayadin cewa, an sami wadanda su ka jikkata.
A garin Humah, jiragen yakin na HKI sun kai wasu hare-haren har sau 10, sannan kuma jiragen sun dauki lokaci mai tsawo suna shawagi a samaniyar birnin wanda ya yi sanadiyyar harin.
A birnin Hums, kafafen watsa labarun yankin sun ce an ji karar fashewar abubuwa masu karfin gaske a kusa da filin saukar jiragen sama na T4. Tashar talabijin din HKI ta 12, ta ce, filin saukar jiragen saman na T4 yana cikin wuraren da aka kai wa harin.
A wani gefen tankokin yakin HKI sun yi kutse cikin yankin Dar’a wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama, da ya zuwa yanzu ba a tantance adadinsu ba.
Tun a 1967 ne dai sojojin HKI su ka mamaye tuddan Gulan, a yanzu kuma bayan faduwar gwamnatin Basshar Asad tana ci gaba da kai wa kasar hare-hare.