Rasha ta gargadi Amurka kan duk wani gigin ka wa kasar Iran hari

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya gargadi Amurka da cewa. duk wani harin soji a kan cibiyoyin nukiliyar kasar Iran zai haifar da “mummunan sakamako” ga daukacin yankin. Sergei Ryabkov ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da wata mujallar harkokin kasa da kasa, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya […]

Burundi ta zargi Rwanda da yunkurin kai mata hari

Shugaban kasar Burundi ya yi gargadin cewa Rwanda na da shirin kai wa kasarsa hari, bayan da sojojin Burundi suka taimakawa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC) a yakin da take yi da ‘yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda. Shugaban kasar ta Burundi Evariste Ndayishimiye ya bayyana cewa, ya samu “sahihan bayanan sirri” da […]

Dakarun Yemen Sun kai hari kan jirgin ruwan yaki na Amurka USS Harry Truman

Dakarun Yaman sun sanar da mayar da martani kan harin baya-bayan nan da Amurka ta kai kan kasarsu, wanda ya hada da hare-hare ta sama har sau 36 a yankuna da dama a cikin gundumomin Sanaa, Sa’ada, da wasu jahohin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkatar mutane da dama. Kakakin Rundunar sojin Yaman […]

Aljeriya ta bukaci taron gaggawa a kwamitin tsaro kan Falasdinu

Aljeriya ta kira taron gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin tattauna halin da Falasdinu ke ciki. Bayan karuwar laifuffukan da yahudawan sahyoniyawa da suke aikatawa a kisan gillar da suke yiwa Palastinawa a yankin zirin Gaza da kuma ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri da sojojin yahudawan sahyoniya suka […]

Ƙasashen Mali, Nijar Da Burkina Faso sun ƙaƙaba wa ƙasashen ECOWAS Kudin Fito

Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen yakin Sahel (AES) mai mambobi uku – Mali da Nijar da Burkina Faso – da ke ƙarƙashin mulkin soja sun ɗorawa sauran kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka haraji na kayakin da suke shigowa kasashen uku. Jaridar Premium Time Hausa ta kara da cewa Sahel ta sanya haraji na […]

Sabbin Hare-Haren Amurka A Kan Yemen Ya Jawo Karin Asarar Rayuka

Akalla mutane 2 ne suka rasa rayukansu a sabbin hare-haren da jiragen Amurka suka kai kan kasar Yemen a jiya Laraba da yamma, saboda hanata tallafin da take bawa falasdinawa a Gaza wadanda sojojin HKI sukewa kissan kare dangi a gaza. Tare da hana abinci shigowa yankin kimani watanni 2 da suka gabata. Tashar talabijin […]

Yau Ce Rana Mafi Muni A Gaza A Cikin Makonni Biyu

Sojojin HKI sun kashe akalla mutane 80 a asbitin Jabaliya a safiyar yau Alhamis, sannan sji ne hari mafi muni da ta kai kan gaza tun bayan da ta sake komawa yakin tufanul Aksa, makonni biyu da suka gabata. Asbitin hukumar UNRWA ta MDD na daga cikin wuraren da yahudawan suka kai  hare-hare a garin […]

AU Tana Shiga Tsakanin Bangarorin Dake  Rikici  Da Juna A Sudan Ta Kudu

 Wakilan kungiyar tarayyar Afirka sun isa birnin Juba na kasar Sudan ta Kudu, a kokarin da suke yi na shiga tsakanin hana komawa yakin basasa. Tarayyar Afirkan ta fara kokarin shiga tsakani ne, bayan daurin talala da aka yi wa mataimakin shugaban kasa Riek Machar a gidansa,lamarin da ya sake jefa kasar cikin zaman dar-dar. […]

Jiragen Yakin HKI Sun Kai Wa Kudancin Lebanon Hari Da Safiyar Yau Alhamis

Rahotanni daga kasar Lebanon sun ce jiragen yakin HKI sun kai hari a garin “Naqura” dake kudancin Lebanon da safiyar yau Alhamis. Jiragen yakin na ‘yan sahayoniya sun kai harin ne har sau uku ajere akan wata tsohuwar cibiyar kiwon lafiya dake cikin garin, haka nan kuma akan wasu gudajen mutane da suke a kusa. […]

 Jiragen Yakin HKI Sun Kai Wa Birane Hudu Na Kasar Syria Hari

Da marecen jiya Laraba jiragen yakin HKI sun kai wasu jerin hare-hare akan biranen Damascus, Hums,  Dar’ada Humah. Tashar Talabijin din ‘almayadin’ wai watsa shirye-shiryenta daga kasar Lebanon ta bayyana cewa; An kai harin ne akan wata cibiyar bincike a yankin Barzah dake arewacin birnin Damascus. Wata majiyar asibiti ta shaida wa tashar talabijin din […]