Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa laifuffukan gwamnatin sahyoniyawa a Gaza sun ketare dukkanin iyakokin kasa da kasa, tare da yin kira da a kawo karshen kashe-kashen mata da kananan yara da makamai masu guba, da yunwa, kishirwa, da cututtuka.
A cewar jaridar Arabi 21, kungiyar malaman musulmi ta duniya ta yi kira ga duniya da ta bayyana goyon bayanta ga al’ummar Palasdinu ta hanyar daukar matakan gaggawa da suka hada da dukkanin hanyoyin soja, tattalin arziki, da diflomasiyya mai inganci.
Dangane da haka ne kungiyar ta yi kira ga limaman masallatan Juma’a a fadin duniya da su sadaukar da hudubar sallar Juma’a na gobe don magana kan wajabcin magance wahalhalu da radadin al’ummar Palastinu da kuma bukatar kawo karshen kisan gillar da gwamnatin sahyoniya ta ke yi wa Palastinawa.
Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta jaddada a cikin wannan bayani cewa, wannan cibiyar ta bibiyi matukar damuwa da bakin ciki da kisan gilla, da laifukan yaki , da yunwa da kishirwa, da kuma gudun hijira da gwamnatin yahudawan sahyoniya tare da goyon bayan ma’abota girman kan duniya suka saka mazauna Gaza a ciki.
Kungiyar ta kuma yi kira ga kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin bil adama da su ci gaba da tallafawa Gaza da kuma tattara laifukan da ake aikatawa har sai an dakatar da harin, da kuma tabbatar da adalci. Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta kuma yi kira da a gudanar da jerin gwano na lumana bayan sallar Juma’a a gobe a dukkanin kasashen musulmi, domin bayyana goyon bayansu ga zirin Gaza da kuma yin Allawadai da ayyukan wuce gona da irin Isra’ila.