Burundi ta zargi Rwanda da yunkurin kai mata hari

Shugaban kasar Burundi ya yi gargadin cewa Rwanda na da shirin kai wa kasarsa hari, bayan da sojojin Burundi suka taimakawa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC)

Shugaban kasar Burundi ya yi gargadin cewa Rwanda na da shirin kai wa kasarsa hari, bayan da sojojin Burundi suka taimakawa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC) a yakin da take yi da ‘yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda.

Shugaban kasar ta Burundi Evariste Ndayishimiye ya bayyana cewa, ya samu “sahihan bayanan sirri” da ke nuni da shirin Rwanda na kai wa Burundi hari, ko da yake bai bayar da karin bayani kan shirin da yake yin zargin a kansaba, wanda Rwanda ta musanta.

“Mun san cewa yana da shirin kai hari Burundi,” in ji Ndayishimiye a wata hira da wata kafar yada labarai yayin da yake magana kan shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, yana mai jaddada cewa “‘yan Burundi ba za su amince a kashe su ba kamar yadda ake kashe ‘yan Kwango, mutanen Burundi mayaka ne.”

Ministan Harkokin Wajen Rwanda, Olivier Nduhungirehe, ya kira wadannan kalamai na shugaban Burundi da cewa “abin takaici ne” ya kuma kara da cewa a cikin wani sakon da ya wallafa a shafin X cewa kasashen biyu sun shiga tattaunawa, bayan da suka amince kan wajibcin kawar da duk wani mataki na soja.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin DRC da ‘yan tawayen M23, yayin da ‘yan tawayen da ke samun goyon bayan Rwanda ke ci gaba da kwace filayensu duk da cewa kasashen biyu na kokarin tsagaita wuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments