Gwamnatin HKI ta sha mamaki da ganin gwamnatin shugaba Trumo na kasar Amurka ta sanya mata harajin shigowar kayakin HK zuwa kasar Amurka, a yayinda, kafin haka ta bada sanarwan cire dukkan kudaden fito ko haraji ga kayakin Amurka da ke shigowa HK.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta majiyar kafafen yada labarum HKI na fadar haka daga bakin wani jami’an gwamnatin kasar.
Labarin ya kara da cewa, Amurka ta dorawa HKI kudaden fito na kasha 17% kacal, sai dai ba abinda take tsammani zai faruba, tsammaninta shi ne irin wanda ta yi wato babu kudaden fito.
Gwamnatin Amurka dai ta rikita harkokin kasuwanci da dama a duniya saboda kudaden fito da ta karawa kusan kasashen duniya gaba daya.