Akalla mutane 2 ne suka rasa rayukansu a sabbin hare-haren da jiragen Amurka suka kai kan kasar Yemen a jiya Laraba da yamma, saboda hanata tallafin da take bawa falasdinawa a Gaza wadanda sojojin HKI sukewa kissan kare dangi a gaza. Tare da hana abinci shigowa yankin kimani watanni 2 da suka gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin Amurka sun kai wadannan hare-hare ne a garin Rasul Isa da lardin Salif a yammacin birnin Hudaida na kasar ta Yemen.
Sannan tashar talabijin ta Almasirah ta bayyana cewa akalla mutum guda ne ya rasa ransa a wannan harin sannan wani guda ya ji rauni.
Har’ila yau jiragen yakin Amurkan sun kai hare-hare kan yankin Qahza a lardin San’aa inda suka lalata motocin mutane, amma babu rahoton rasa rai a yankin. Sannan sun lalata ma’ajiyar ruwa na yankin Sa’ad inda suka hana kauyuwa da dama ruwan sha.
Majiyar ma’aikatar lafiya ta kasar Yemen ta bayyana cewa tun watan maris da ya habata jiragen yakin Amurka sun kashe mutane kimani 60 a kasar Yemen, sannan wasu 139 suka ji rauni.