Rasha ta gargadi Amurka kan duk wani gigin ka wa kasar Iran hari

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya gargadi Amurka da cewa. duk wani harin soji a kan cibiyoyin nukiliyar kasar Iran zai haifar da “mummunan

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya gargadi Amurka da cewa. duk wani harin soji a kan cibiyoyin nukiliyar kasar Iran zai haifar da “mummunan sakamako” ga daukacin yankin.

Sergei Ryabkov ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da wata mujallar harkokin kasa da kasa, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai wa Iran hari idan har ta kasa cimma matsaya da Washington kan shirinta na nukiliya.

Ryabkov ya ce, “Hakika ana jin barazanar, ana kuma jin bayanai kan abubuwan da suka dace,” in ji Ryabkov, yana mai cewa “Sakamakon hakan, musamman idan harin ya kasance kan kayayyakin nukiliya, na iya zama bala’i ga daukacin yankin.”

Ya ce sabbin kalaman na Trump za su kara dagula al’amura ne kawai da kuma rikitar da lamurra dangane da sha’anin Iran.

Ya kara da cewa, “Muna daukar irin wadannan hanyoyin da ba su dace ba, a matsayin wata hanya da Amurka ke bi domin cimma muradunta ta hanyoyin da basu dace ba, kuma sun saba wa ka’ida da doka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments