Aljeriya ta kira taron gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin tattauna halin da Falasdinu ke ciki.
Bayan karuwar laifuffukan da yahudawan sahyoniyawa da suke aikatawa a kisan gillar da suke yiwa Palastinawa a yankin zirin Gaza da kuma ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri da sojojin yahudawan sahyoniya suka yi a yammacin gabar kogin Jordan, Aljeriya ta bukaci gudanar da wani taron gaggawa na kwamitin sulhu kan halin da Falasdinu ke ciki.
Kasar Aljeriya ta ba da misali da karuwar hare-haren da Isra’ila ke kai wa a yankunan Falasdinawa da ta mamaye musamman a yankin zirin Gaza a matsayin dalilin bukatar gudanar da wannan zama. Sama da wata guda kenan da Gaza ke cikin wani mummunan yanayi, ana kashe jama’a ciki har da ma’aikatan agaji.
An kuma gabatar da wannan bukata bayan gano gawarwakin ma’aikatan agaji 15 da ma’aikatan jin kai da daukin gaggawa a Gaza wadanda ke da alaka da kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu, da kungiyar kare fararen hula ta Falasdinu, da kuma Majalisar Dinkin Duniya.
An kuma bayyana karuwar tashe-tashen hankula da ‘yan sahayoniya mazauna Yammacin Kogin Jordan ke haifarwa a matsayin wani dalili na neman wannan taron gaggawa.
A zamansa na 58, Kwamitin Kare Hakkokin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da wani kuduri kan halin da ake ciki na kare hakkin bil’adama a yankunan Falasdinawa da suka mamaye ciki har da gabashin birnin Kudus .
A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, an amince da kudurin ne a ranar Laraba inda kasashe 27 suka amince, 4 suka nuna adawa, sannan kasashe 16 suka kaurace kada kuri’ar.